Kishore Kumar Hits

Umar MB - Rabuwa şarkı sözleri

Sanatçı: Umar MB

albüm: Rabuwa


(Kiso ni domin Allah)
(Ki kini domin Allah)
(Ba don ra'ayi ba)
Rabu dani tafi kije ki
Karki bini
Magani naso nasha ya ishe ni
Misali zan kafa zuwa wani karni
Wanda ke yin so za'a masa bayani
Matsaloli na dake sunata kara muni
Yanzu babu so a zuciyar mu nasan kin sani
Hadarin so yana da muni
Baya hawa kan mizani
Da kwakwalwa nai tunani
Babu so a zuciya

Nai riko da gaskiya baki shaida ba
Rayuwar da zaki yi ba zana hana ba
Idan so tekune ba zamu guje ba
Mun fada cikin sa ba muyi nasara ba
In so tsun-tsu ne bazai motsa ba
Dan ba fuka fukin sa bazai lula ba
Idan so na magana ba zai waka ba
Muryar ta sarke ko bata washe ba
Bugu zuciya take yi
Niko kin sani layi
Kin saka ni sahu na bayi baki tausayan ba

Babu so cikin zuciyar ki kin fada min
Na gani da idona domin kin shaida min
Kunnuwa sune sila, sune suka jiyo min
Idanu sun shaida domin sun gano min
Zana barshi so
Duk da ban shirya ba
Kiso ni domin Allah
Ki kini domin Allah
Ba don ra'ayi ba

Поcмотреть все песни артиста

Sanatçının diğer albümleri

Benzer Sanatçılar