Kishore Kumar Hits

Umar MB - Dena kulani şarkı sözleri

Sanatçı: Umar MB

albüm: Dena kulani


Dena kula ni
Dena beye ni
Dena kula ni
Karka beye ni
Sha kurumin ki, yar yariya babu batun so dani dake
Dubi maza na jiran tsamani kin bar dai dai dake
Karda ki bini karda so ni jeki gurin dai dai dake
Ban baki fuska sai ki farka babu harka ja da baya
Daina kula ni
Karka beye ni
Ka dubi kalabi tsakanin rauna ni giwar mata ce
Ka tsaftace dukan kalamanka saurayi don karda ka kauce
Kwarya taje ta nemi kwarya in ta bi akushi zata rushe
Ina da kyau kasa ido dubi deresin nan ina tushe
Ka nemi warin, ka nemi dai dan ka gaskiyar haka take
Babu ni, ba ka, bani kallon ka, bani bin hanyar duk da kake
Zubi da kyunka koko nasabar ka, kar su saka ka zake
Karka ja, ja in ja, babu ni ba ka a soyayya
Dena kula ni
Karka beye ni
Karka kula ni
Karka kula ni
Ki sauke dukan abunda ke ranki don ko soyayya ce
Zan zana sunana a cikin zuciyar ki don karki mance
A zahiri na da badini sanki ban bada rance
Ina dakon soyayyar ki, ban kaunarki in adana
Karka kula ni
Karka beye ni
Awarwaro adon mata koko azurfa
Idan nazo gabanka na zauna sai kayi mini rumfa
Idan na saba ma saurayi to sai ka tina fa
Ina ado ne domin ka, kar kai shakka kaine zabina

Поcмотреть все песни артиста

Sanatçının diğer albümleri

Benzer Sanatçılar