Kishore Kumar Hits

Hausa Soundtrack - Kawayena şarkı sözleri

Sanatçı: Hausa Soundtrack

albüm: Kawayena


Kwana na ya kusa karewa
Nima kwana na ya kusa karewa

(Mai salati on the beat)
Kwana na ya kusa karewa, ammah a gidan mu zan tafi daki na
A gidan mijina zan rayu zaman kadaici ya kusa yankewa
Kwana na ya kusa karewa, a gidan mu zan yi farar mata
Kiji sai dake ni zan rayu, abokanai na sun gama shiryawa
(Allah sassaka)

Na gane wacce bata da mai son ta, jaje gare ta dole a mika shi
Buri na raina ya cika, Allah ya nufa zaman gida zan rabu dashi
Aure na zanyi, can a gidana abinda na so zan dafa naci na koshi
Da nasan hakane shekara 15 cikin gidan mu ba zan so nayi ba

Kawaye na kuzo ku taya ni murna, yau saurayina ya kawo lefe
Kuyi rakiya muje gun ummah da abba kuskuren da nayi su yayyafe
Zan bika sau da kafa da soyayyah, kuruciyar mu har ta ishe tsofe
Ko ba'a abinci, babu gida sutura ta kwalliya ba zanki biyayya

Ayi min kitso, sannan ayi min kun shi, labba ka duba na saka jan baki
Kaga shigar da nayi maka na shirya, na saka santi harda sudan baki
Muyi alola muyo sallah mu wuce, gobe da safe kaga rawar baki
Farin ciki da murna wacce nake, nice silar da zaka zamo babba

Sha kurumin ki tunda ina sonki, alkawari bazan ki na damke ba
Kuma a rai, akwai wani sirri toh ammah a yau bazan ki na bude ba
Aure martaba ne shike sanya kankani a gobe ya zam babba
Ai yau fah kai kayi min kyautar da tasa akan ta toh ba zana ji kunya ba

Nayi godiya a gurin ku abokaina, kunyi halacci nima shaida ne
Allah ya tabbatar mana alkhairi, sannan ya kaimu ranar kowanne
Duk addu'an da zanyi tilas na saka ku a cikin a daren alkhairi ne
Na dandana a cikin raina, jina nake kamar ba nine ba

Поcмотреть все песни артиста

Sanatçının diğer albümleri

Benzer Sanatçılar