Kishore Kumar Hits

Hausa Soundtrack - Ni Na Yarda Da Hubbina şarkı sözleri

Sanatçı: Hausa Soundtrack

albüm: Ni Na Yarda Da Hubbina


(Sona ne fah, on the beat)
Hello baby?
Ya masoyi (na'am)
Ina jiran ka (toh)
Kazo da sauri, zuciyata tana mini dinlin-dinlin
Gani nan tafe (da gaske?)
Bazan jima ba (toh)
Zan zo na ganki, domin kada zuciya tayi dinlin-dinlin
Uhmm-uhmm-uhmm
Baby zuciya na dinlin-dinlin
(Sanity Production)
Ni na yarda da hubbi na, baby na
Safe da son ka na karya kumallo
Auren ka shine burina, lissafi na
Sauran kawaye nayi masu gwalo
Kyakkyawa na dan taso, in dan baka azurfa
Marmarin ka nake ko yaushe kamar talgen shinkafa
Dan miko hannun ka, masoyi na muyi tafa-tafa
Muyo aure watarana na haifo ma yan dinlin-dinlin

Mai kyawun asali, farin ki foreign ne ba powder
Gashi kina kyalli, fatar jikin ki kamar wani tsada
Burina shine auren ki, idan kin yarda
Sadakin ki koda nawa ne, na yarje zan bada
Don haka ke na rike
Soyayyah ba sake
Kema karki sake
Ki bani anan take
Kina tafe gani a bayan ki, kamar tayan keke
Son ki a raina ya zauna yana mini dinlin-dinlin

Ranar wanka ba'a boyan cibi zan bude sirri na
Zancen Gizo baya zarce na Koki fada mini hubbi na
Ni jariri ne a wajen ki sai kinyo raino na
Ba zana bari kayi kokawa ba zan baka ruwan kauna
Kan soyayyah na dace ba za'ayi mini gori ba
Kai ke sosa mini raina in yana mini dinlin-dinlin

Mmm dinlin-dinlin

Поcмотреть все песни артиста

Sanatçının diğer albümleri

Benzer Sanatçılar