Kishore Kumar Hits

Hausa Soundtrack - Ranar Baiko şarkı sözleri

Sanatçı: Hausa Soundtrack

albüm: Ranar Baiko


(Sugar on the beat)
Ranar baiko kaga ba za'a ki ce mini amarya ba
Wanda nake so ya gama min komai rufe ni asiri na
Tunda na samu kamar ki nasan cewa bazan dada kuka ba
Kinga da gaske nake kaunar ki a rai bazan miki tamka ba

Na ishe girma abba na yace zai yimin aure
Dawa nafi so na fada masa kaine zance kuma ya kare
A kaini gidan ka da kunya ta, ranar sai na daddaure
Abinda ka so shi zan maka ango na taho mu rufe kyaure
Kaga irin kallon da kake mini ya za'ayi in jure?
Aure aljannar duniya, marashi bata more gata ba
Ya bata more dadi ba?

Taho shiga kofar zuciya zan bude miki ban saka dan murfi
Idan na gano ki koda a jiki na nakan samu dadin karfi
A gan mu a bar mu dake haka inji ruwa yace wa da dan kifi
Idan kika barni abin da ya kyautatu a sani ciki yafi
Kin zarce mata a ado na shigar ki nace miskila ai mafi
Kisa haka ranki abinda kika yi mini to bakya yi a banza ba
Bakya yi a banza ba

Ranar baiko na nayi shiri domin na burge masoyi na
Ni zan ji dakai tamkar yaro dan shekara daya butty na
Kai zan wa ado a gaban ka na zo inyo fari da idanuna
Wanda bata da tamkar kai bata more kuruciyar ta da kauna ba
Lallai bata more kauna ba

Ka jani ka kai ni mu hau kan lilo
Abin kasa kin tono
Ka kai ni ina sha'awar shan Milo
Dubarar na gano
Ka tuno da zaman mu da safe a parlour
Naje ta garin gano
Dadin rayuwata in bakai ba zana ji shi a daidai ba

Ranar baiko kaga ba za'a ki ce mini amarya ba
Kinga da gaske nake kaunar ki a rai bazan miki tamka ba
Ya bata more dadi ba?
(Sugar nest)
Tunda na same ki kamar nasan cewa bazan dada kuka ba
Wanda nake so ya gama min komai ya rufe ni asiri na

Поcмотреть все песни артиста

Sanatçının diğer albümleri

Benzer Sanatçılar