Kishore Kumar Hits

Umar M Sharif - Amana şarkı sözleri

Sanatçı: Umar M Sharif

albüm: Tribal Grooves, Vol. 22


Ayyeah
Amana ki bani inda yarda
Soyayya a kan hakan take yin karko
Amana ka bani inda yarda
Soyayya a kan hakan take yin karko

Dadin bacci ke saka ayo minshari
Ita wuya ko sai tasa ayo kakari
A kallo ko a gane yanda nake a tsari
Alamu sun nuna babu sauran buri
Indai zanyi rayuwa dake
Masoya cikin su za na zama na farko

Tukwuici na so ka bani kauna yafi
In boye a zuciya na sa mai murfi
Cikin raina ka riga da kayo karfi
Ka kai matsayin da baka yi mini laifi
Amanar da ka bani na rike
Idan ka kira ni ba jira zan sheko

Kina kyau da kallo, idanun gani na
Idan kinka bullo, sun koma
Tufa yafi yalo, abin marmari na
Sai nayi musu gwalo, in rama
Kina nan ba abinda zana nema
A fanin so ba abinda zai mini tsaiko
Amana ka bani inda yarda
Soyayya a kan hakan take yin karko

Amana ki bani inda yarda
Soyayya a kan hakan take yin karko
Dacewa cikin so, nina fi kowa
Masoyin dana so na kama
Duk inda ya doso, yakan burge kowa
Baya yimini kwafso haka nima
Na zabe ka bani babu rama
Faranta maka rai zan dada in ninko

Amaryata zani baki suna
Mijina ango idan da kwana
Za nayi murna inga wanga rana
Za nayi kuka daga cikin idona
Kukan dadi ne abin nufi na
Nima zanyi hakan dani dake muyi anko

Amana ki bani inda yarda
Soyayya a kan hakan take yin karko
Soyayya a kan hakan take yin karko

Поcмотреть все песни артиста

Sanatçının diğer albümleri

Benzer Sanatçılar