Kishore Kumar Hits

Umar M Sharif - Ya Rasululah şarkı sözleri

Sanatçı: Umar M Sharif

albüm: World Rhapsody Vol, 17


Ya Rasulallah
Manzo na fiyyayen halitta
Kai nake yabo
Wanda yabika ya rabauta
احداحد
Rabbi kai na kira a fari
الله الصمد
Kaine kayi duhu da nuri
لم يلد و لم يولد
Mai kyauta wanda Baya gori
Rokonka nake
Rabbana dada man fahimta
Kai kake mana
Mu kau ba abinda zamu maka
Kayi ruwan sana
Ga kasa ka shinfida mu taka
Ga iska nan mushaka
Ga dabbobi domin mu yanka
Kayi ni'imomi a garemu da basu misalta
Gani kai tsaye zan fada cikin yabon rasula
Babu waiwaye na toho gurin abban batula
In ka rungume ni lahira ban zubarda kwalla
Kai ne mai cheto na inuwarka zan so in shige ta
Hasken da ba duhu har cikin sa mahmudu kaine
Kamshin da yayi kamshi ko turare asalinsa kaine
Hanyar kace a mike duk sabaninta hadari ne
Wanda ya ki ya bita
Lahira shi za ya jigata
Karshe azzuhuru kozulun asalinsa shine
Komai ya mallaka yin kyauta ya zamo jikine
Komai ya ambata furucinsa duka ilimi ne
Sun maka lakabi da
الأمين dan tsantar aminta
Duk girman arziki in yazo gabanka matalauci ne
Duk ilimin mai ilimi in yazo gabanka jahili ne
Duk gatan mai gata in akwai ka almajiri ne
Na dau kokon bara
In ka zuba mini zani huta
Ka haska duniya nakane ya ke zuwa garemu
Anyi an gama kamar ka Wallahi ba'a samu
Mu kai muka rike tsani wanda zamu hau ya kaimu
Jamu zamu bi aljanna muje mu kwanta
Dan gatan rabbi ne duka abinda ya roka za'a bashi
Shine ya yi addu'a in ba dan shi ba babu nishi
Mai dumbin masoya
يا كريم da ba kamar shi
يا امام الرسول
سيدنا baban fatima binta
يا ايها المدثر
Mai cikkakiyar sifa da zati
Kayi sammako wanda zayazo sai dai a latti
Kai ne wanda da Allah da mala'iku suke yi wa salati
In mun shiga lemarka babu sauran abin bukata

Поcмотреть все песни артиста

Sanatçının diğer albümleri

Benzer Sanatçılar