Kije dani dukka inda zaki Kice dasu, "Ga wanda zaki aura" Kaje dani dukka inda zaka Kace da su, "Ga wacce zaka aura" ♪ Na tsallako ina ta waige-waige Idanuwa ke suke ta hange Ga zuciyata tana ta bege Sautin ki shi nake sakawa goge Rawa nake tayi gaban ki na dage Ki walwala shine farin ciki na nima ♪ Na ambato kai nake ta zance Kaine daya bani kauce-kauce Ina da kai mai zana yo da rance? Nagode Allah samun ka ni'ima ce Cikin kawaye ni suke ta zance Suna ta barka har suka bani sandar girma ♪ Kwalliyar ki duniya ta haska Kama da hantsi ko'ina ya leka Daban da damina da ita da kaka Albarkacin ki bai dama iyaka Jirgi na hau gidan ki zana sauka Ina da tabbacin zaki mini tarba nima Kaje dani dukka inda zaka Ka ce dasu, "Ga wacce zaka aura" ♪ Kije dani dukka inda zaki Ki ce dasu, "Ga wanda zaki aura" Kaima ka tabbar, ina ji da kai Dangina sun sani, gare ni baya kai Soyayyah tayi kyau, hadin mu ni da kai Ba sauran damuwa domin ina da kai Kowa ya sani cikin son ka yanzu na sa kai Na nutsa kafin a gan ni asha fama ♪ Sunan ki koda yaushe shina ambata Dake kadai nake zuwa in zani shakata Na taho gare ki, karki ce in dakata Kece malama ki rubuta in karanta Kowa ya shaida nifa nayi mata Ku daina fadin aibu nata tunda na zama kurma Kaje dani dukka inda zaka Ka ce dasu, "Ga wacce zaka aura"