Kishore Kumar Hits

Umar M Sharif - Matan Aure şarkı sözleri

Sanatçı: Umar M Sharif

albüm: World Rhapsody Vol, 23


Matan aure iyaye
Kamannin mu da ke da idanu na gani
So yabi jini farin ciki na kece
Kamannin mu da kai da idanu na gani
So yabi jini farin ciki na kaine
Kece kinka zama farin cikin aure
Ki zauna zuciyata in rufo kyaure
Muyi wasa ba fada taho muyo tsere
Ki daura ni a hanya kinji in nayi kure
Nina yarda zama dakai koba jere
Akwai babu na yarda haka zan jure
Da dadi, da wuya hakan muna tare
Mai son ya nufe mu da sharri Allah ya tsare

Kece farko a cikin raina nayi ajewa
Mata duka kin fisu guna baki da tamka
Kaine farko a cikin raina nayi ajewa
Zo kaban zoben zinare, ni in baka azurfa
Ke kadaice gaki cikin rai babu wacce nake gani
Rabin jikina inba kai ko a zahiri sam babu ni
Ko'a runduna kece ta daban kinsha gaban su da kwarjini
Cuta ta so da tayi mini kamu kai kayi mini magani
Kin sha gaban su a kwarjini-kwarjini-kwarjini
Kaine kayi mini magani

Kece sarauniya
Na baki zuciya
Kece guda daya
Duniya ta masoya
Nice sarauniya
Na baki zuciya
Kaine guda daya
Duniya ta masoya
Sam babu shamaki waye zai min?
Birki a son ki babu mai taka min
Uwargida-amarya, ake ce min
Kaine mijina ni kadai ba mai kwace min
La-la-la ki daina fargaba
Koda da yan daba
Karyarsu su rabani ni da ke uwargida

Bayan ke a zuci babu kowa
Uwargida ta daga ke na rufe
Bayan kai a zuci babu kowa
Miji na aure mai sani farin ciki
Ni ke nake gani ko cikin mafarki
Duk wanda ya taba ki zani dau mataki
In killace ki in saka cikin akurki
In baki kula don kin zamo mata ta aure
Na dace so
Na more so
Na samu a sauki
Na shuka so
Na girbe so
Yau gani a daki

Поcмотреть все песни артиста

Sanatçının diğer albümleri

Benzer Sanatçılar