Soyayya tayi mamaya tayi caraf ta kama mini zuciya Na samu saurayi madubin duba ya zan na furta Ki duba, madubin dubawa Ki furt mai soyayya ♪ Wayyo, yau na afka cikin tarkon soyayya na wani saurayi Kyakkyawa mai kyau na hali ammah na rasa yanda za nayi Nayi nisa cikin kaunar sa babu wani misali da za nayi Da zai so ni bani da damuwa sai farin ciki Tauraro na ♪ Shawara ta ki furta mai yanmata ki daina jinkiri Domin kisan cikar matsayin ki a gun shi zaifi tsari A bari ya huce shike kawo rabon wani sai kiyi hanzari Ikon Allah kila ki dace, ki jaraba kinji yar'uwa ♪ Saboda soyayyar da nake masa bana bacci cikin dare Da rana ban iya komai sai tunanin sa har cikin dare Sai nayi yunkurin na furta kunya sai tasa na kakare Ina tsoron kar inyo tufka ta karshe ya warware ♪ Musulmin kwarai an san shi da tawakkali a cikin rayuwa Misali na kasuwanci yau riba, gobe kuma faduwa Da zaki yarda da wannan a duniya bake babu dimuwa Allah kasa mu dace a duniya har da lahira ♪ Wai-wai-wai Ashe so haka yake yasa na kasa natsuwa Ina tare dashi na nuna mai yaki fahimtuwa Yakamata shi da nake so ya fahimce ni ko ta idanuwa Waye zai ce yana sona in amsa mai yaji dadi ♪ Ki duba, madubin dubawa Na samu saurayi madubin duba ya zan na furta Ki furta mai soyayya Soyayya tayi mamaya tayi caraf ta cafke mini zuciya Na samu saurayi madubin duba ya zan na furta