Kishore Kumar Hits

Umar M Sharif - Jininjikina şarkı sözleri

Sanatçı: Umar M Sharif

albüm: World Rhapsody Vol, 25


Da ganin ki sai na kamu
Gashi kin zamu jinin jikina
Lokaci guda na kamu

Aha-aha-aha
Aha-aha-aha

Kallo daya bisa ka'ida nayi miki
Zuciyata sai ta kamu yan mata
Shi biri da ba'ayi mar gada
Gani nazo a gareki sannu-sannu yar gata
Ban zo da matsala ba
Ban zarce ka'ida ba
Ki min iso nazo gun ki tunda kinga bako
Shi ba abin gudu ba

Na amsa sallamar ka taho ga mazauni
Ka furta zantukan ka
Al'umma rahama ce harda kai ciki
Yaka-yaka ban gudun ka
Manufarka ban sani ba
Ban gani cikin ido ba
Ni dai fata nake komai zan ji
Ya zamo alkhairi ina maraba

Ba ki gane me nake ta nufi ba
Soyayya ce nazo da ita, da ita, da ita
Kallo daya da nayi miki
Na samu macen da nake so nayi gamo da ita, da ita, da ita
In jira bazan iya ba
Zantukan da nayi ki duba
Soyayya ce nake so ki bani
In na samu zan rike bazan saki ba
Aha-aha-ahaa
Aha-aha-ahaa

Na yarda, na yarda, na amince
Ni da kai taho mu kulla
Tsarin ka, lafuzan ka su suka sace zuciya, ruhi jimulla
Bazan guje tayi ba
Nayi charaf son ka na karba
Ni dakai kawai mu faro soyayya sabuwa
Karshen ta nada riba

Nagode, nagode, nayi murna, mai zan biya tukuici?
Ba komai, ba komai, tunda ka yaba so ne shine tukuici
Lallai nazo da sa'a sai hamdala, kinyi min karamci
Soyayya ce ta sanya
Komai bazan gaza ba

Поcмотреть все песни артиста

Sanatçının diğer albümleri

Benzer Sanatçılar