Sadiq Saleh production Albarka cikin so a yau na samu Kyakkyawa sanyin zuciya Ke na aza akan kadami na halacci Cuta ba matakin ki ba Albarka cikin so ashe na samu Kyakkyawa sanyin zuciya Kai na aza akan kadami na halacci Cuta ba matakin ka ba ♪ Ayah-ayah-ayah ♪ Wacce naso a raina a yau ta so ni Na more Duk kunci dake zuciya ta kore Ta kore Babbu kamar ta na jaddada ita dai ce Na ware Duk inda nake tana nan ashe ba zance bane Ashe zuciya ta riga da tai mata babban gurbi Ayah-ayah-ayah Baka da damuwa, zan baka mayafi A halifin cikin ruwa, sai an saka kifi Ni da kai kwai shakuwa mai tsananin karfi Mun tsunduma kogin so, mai zurfi Nai maka shimfidar fuska tafi ta tabarma Tunda a yau kai power daga hannun dama Kai tafiyar ka harda izza ka riga ka girma Na riga nayi kas da gwiwa tamu ta yan mata Oh oh oh Ummm, oh oh oh ♪ Na shiga damuwa, ban gan ki ba baya Abin jin tausayi, yanayi na maraya Gashi kin lailaye zuciya, ah kin shiga kurya A tafi kankani, su sun baki masoya (Kai haba) Soyayya kike mini kwando-kwando Talatsu ne wanda ya wanda yake tsoron dodo Kaunar ki ai ta ishe ni har riga, wando A yanzu ko ba abinda zai sa inji tsoro Kaii! Danyi kirana zana zo da wuri Ka bani umurni zanyi ba jinkiri Naki silalla dakai nake fahari Masoyi kana kyau kuma ka kara fari Mata ni nace maku kwalele-kwalele Nida masoyina alaka ta bulle Jirgin kauna zo mu shige sama mu shille Rashin masoyi fitar sa a zuci azaba