Sadiq Saleh's production Wayyo ni Allah naga wannan zamani Ga ungulu tayi zaman kitso gashi a batta da ♪ Kai mai bidar labari Toh sai ka matso kaji Wanda duk ya fito bida Mai furcin ya gaji Ga mutanen duniya Na ta neman agaji Burin wani bai wuce Tona sirri don a ji Nagano mata da yawa Tsallakan ta a jan aji Bangaren wasu sai jiya da masu karyar arziki Wayyo ni Wayyo Wayyo Allah Wayyo ni Wayyo Wayyo Allah ♪ Toh ashe duniyar ga komai rabbi yai masu wa'adi Rayuwa kaddara ga kowa Zata zo bisa sanadi In muna so cin ma tsira Sai mu koyi mujaddadi In mu kai shukar kwarai Morar ta zamuyi har badi Sai mu kara riko da bauta Gun sa Sarki ahali Mi biyayya gun manya manya dan mu samu tabaraki Wayyo ni Wayyo Wayyo Allah Wayyo ni Wayyo Wayyo Allah ♪ Rabbi kai kai mun nufin waka Kai mini arziki Sai tazam sana'a A hakan wadansu suke mani dan baki Neman halali na nakeyi Ya zan ci wa wani hakki Tsari tsarin ilahu shi ke tsare dukkan dare Nabi uwata nabi ubana ibada na rike Rabbi kayi mini daffa'i Sannan kayi mini jallabi Duk wani mai shirin sharri a kaina bazai cin ma ba ♪ Wayyo ni Wayyo Wayyo ni Wayyo Ka ci hakin wani (wayyo Allah) Ka ci hakin wata (wayyo Allah) Ka jefai wani (wayyo Allah) Ka jefai wata (wayyo Allah) Ka shaike wani (wayyo Allah) Ka shaike wata (wayyo Allah) Kai kazafin wani (wayyo Allah) Kai kazafin wata (wayyo Allah) Kai fyade haka (wayyo Allah) Kai garkuwa haka (wayyo Allah) Ba tsoro haka (wayyo Allah) Ginin karshe naka (wayyo Allah) Da kai da ubangiji (wayyo Allah) Babu yai agaji (wayyo Allah) Kai da hanlinka ku rabu jikinka barai naka wayyo Wayyo ni Wayyo Wayyo ni Wayyo Wayyo ni Wayyo Wayyo ni Wayyo ♪ Sadiq Saleh ne