Kishore Kumar Hits

Abdul D One - Zo Kiji şarkı sözleri

Sanatçı: Abdul D One

albüm: Zo Kiji


(Ad music studio)
(Yarima on the beat)
Zo ki ji labarina
Abinda yake a cikin raina
Zo ka ji labarina
Abinda yake a cikin raina

Daga bakin yan yara na san sunan ki
Na dade da karantar ki da ma halin ki
Na dade da fahimtar dukka dabi'un ki
Kowa nayi tambaya kan ki zai yaba halayen ki
Hakan ya sa ni ina jin wani shauki
Wanda bai misaltu, a fuska ta kadai za'a gane

Nima da halin ka nayi zane
Samun ka gare ni dabara ne
Haduwar mu da kai wani sirri ne
Ba kowa bane zai gane
Zuciyar ka garen kyakkyawa ne
Kai min shaidar kirki dole ni nima zanyi ma

A cikin kalamin ki akwai kauna, duka na saurara
Nayi bibiya ba gyara, komai kin tsara
Ke har harda abinda nake so shima kin kara
Da akwai wasu ki tattaro ki adana su duka ki tattara
A tsakanin mu ba abinda ya rage balantana saura
Komai yayi daidaita sai mu fara sanar wa mutane
Zo ka ji labarina
Abinda yake a cikin raina

Baka da tsara wanda yake binka
Koko ya gane akidar ka
Har yayi tunanin shigowa gonar ka
Koda kasa ka tsallake, ina nan bayan ka
Duk inda zaka je, ina bin sahun ka
Koya kayi nisa dani, ina jin kewar ka
Ko'ina sassan jiki sunan ka ya kama
Zo ki ji labarina
Abinda yake a cikin raina

Поcмотреть все песни артиста

Sanatçının diğer albümleri

Benzer Sanatçılar