Auta Waziri kuke ji malam Prince production Na soki, kin so ni bazan so ki butulce ba Na saba, da ganinki bazan rintsa idanu ba Alkairin ki na tuno bazai gogu a raina ba Hasken ki yana nan zahiri ba zaya disashe ba ♪ Na saba inji bayanin ki tun a karon farko Ta yadda kike nunan kauna ko nayi sama zama zan sakko Koda na hangi alama kece ka dadan karko Na so ne in cika burin ki ba daga baki ba Ahh, ba daga baki ba ♪ Allah shine mahalicci, mai iko duka kan kowa Abinda yaso, in har ya nufa ba mai chanzawa A cikin kudurar sa yake kyauta bamai kwace wa Idan ya kashe ba mai rayawa tuni nayi farki Allah Allah mun gode maka ♪ Nidai nasani ina kaunar ki a zuci ne da bakina Idan har nayi akasin haka na raina iyaye na Da bukatar in kula ne dake har ya tsawon raina Ammah kuma in Allah bai so ba ma yafe juna Na soki Na so muyi aure ♪ Kin san ke 'ya mace ce mai kima bazan ki kwantace ba Akwai ki da tsoron Allah zahirin ki nake duba Karki yarda ki dauki batun da ba zaiyi kyawun karshe ba Bawai don gina soyayyah ta zan fadi wanan ba ♪ Nasoki, kin soni bazan so ki butulce ba Na saba, da ganin ki bazan rintsa idanu ba