Kishore Kumar Hits

Nura M. Inuwa - Zeenat şarkı sözleri

Sanatçı: Nura M. Inuwa

albüm: Ma'aurata


Eh, mai kwalliyar jiki Zina fara hasken idaniya
Rayuwa ta duniya sai hakuri, karki duba zamani
Eh, sai sannu sannu dan Zinatu ni na fara nazari
Rayuwa ta duniya sai hakuri, na kyale zamani
Komai da lokaci, Zinatu so na wanda yai daban
Mai san yayo fice yayi hakuri zai zama adon gari
Eh, kauna a kwaikwayo zana fado so ne ruwan jiki
Kiyi tankaden ki Zinatu ki dau gari ki bar tsaki
Bayan ki na tsaya zaniyi kuka in kina hake
Mugun riko ake miki gida nuna su na nagani
Komai da lokaci, Zinatu so na wanda yai daban
Mai san yayo fice yayi hakuri zai zama adon gari
Eh, yau ni a rayuwa nayi ganin sauyi na yanayi
Cuta ake tayi man a gida ba yadda zanayi
Ba wanda zaya nunan kauna ya aje ni dausayi
Kuka na zuciya na dattuwa, dan zasu fad dani
Komai da lokaci, Zinatu so na wanda yai daban
Mai san yayo fice yayi hakuri zai zama adon gari
Duk wanda rabbi yai wa baiwa toh zaya sha wuya
Hujja abar rika Zinatu kina fama da makiya
In kin chi jarabawa gaba zaki zamo zinariya
Ni ina da tausayi naki a rai ba yau ba tuntuni
Komai da lokaci, Zinatu so na wanda yai daban
Mai san yayo fice yayi hakuri zai zama adon gari
Komai da lokaci, Zinatu so na wanda yai daban
Mai san yayo fice yayi hakuri zai zama adon gari
Eh, gata na tashi gun Umma da Abbah na sun ban kula
Da akwai su rayuwata kuma waye zaya dagula
Gashi na zama kamar baiwa na rasa kula dab dala
Mutuwa ta haddasa, na rasa chanjin mai kula da ni
Komai da lokaci, Zinatu so na wanda yai daban
Mai san yayo fice yayi hakuri zai zama adon gari
Eh, taso ki daina kuka mana Zinatu yar marainiya
In ran ki yayi dachi daurai ki tino hawainiya
Girman ta kinga tayi shi iyayye babu duniya
Chanjin kala takeyi in tafito sai anyi sansani
Komai da lokaci, Zinatu so na wanda yai daban
Mai san yayo fice yayi hakuri zai zama adon gari
Eh, kaiman zanchen da ya san natsuwa rai na na sanyaya
Kai daya nake gani fuska fari ga yar manuniya
Maganar da kayi min ta shiga kunnai ba hatsaniya
Sarkin mu zai duban lamari sauki da zandami
Komai da lokaci, Zinatu so na wanda yai daban
Mai san yayo fice yayi hakuri zai zama adon gari
Eh, mai kwalliyar jiki Zina fara hasken idaniya
Rayuwa ta duniya sai hakuri, karki duba zamani
Eh, sai sannu sannu dan Zinatu ni na fara nazari
Rayuwa ta duniya sai hakuri, na kyale zamani
Komai da lokaci, Zinatu so na wanda yai daban
Mai san yayo fice yayi hakuri zai zama adon gari

Поcмотреть все песни артиста

Sanatçının diğer albümleri

Benzer Sanatçılar