Salim Smart on the beat ♪ Ye, kan abinda kake so Baka fiye ganin aibu ba So yamin bazata, yasa ina fargaba Wasu sun ce hali sai yazo daya, ake zama Ni kuma nayi musanta hakan ina tantama So kan canza hali, kokarin ayin um'ma Tunda shi kadai ne ke sarrafa zuciya ♪ Ye, da so kama ne, koko dan Adam ne Ba zana bari ya shige mini zuciya ba Daga kanka naga ne, so hadari ne Kuma wajibi ne, bamu tsallake ba Halin ka ba zai sani in guje ka ba Addu'a nasan ba abinda bata barshi ba Rai da zuciyata basu san wanin ka ba Taya ido zai runtsa bai ganka ba Inna rusuna maka, ba don niba Duk wanda yayi sama, ka gyara hali Zan kyautata maka, in da dada Komai inyi maka, ba gajiya ♪ Ye, akan sonka duba, yarda nabar hayyaci na Bani gane komai, a dare ko Kuma da rana Ba zana bari ba, koda zan rasa raina A cutar da kai, hakan shine kudirina Taimaka min na samo sukuni Zuciyata ko ta daina rauni Tallafa min, kokwanto ya barni Inji dadin zaman duniya Koba don niba, da akwai yan uwa Ko babu su, kasan akwai mutuwa Ga kwanaki suna sake raguwa Ga shekaru suna kara hauhawa ♪ Ehh, kowanne dan Adam akwai kaddaran shi Kowanne so da akwai silar faruwar shi Duk wata zuciya tana dauke da tabon shi Nima tawa duba akwai irin shi Ko kiso, ko kar kiso naki ne ni A zuciyar ki, babu kowa kamar ni Tunda so har ya shigo tsakani Kibar tunanin zani canza hali Ko mutuwa, bata raba mu ga misali In babu ke, ya zan yi rayuwa?