Kishore Kumar Hits

Salim Smart - So Kenan - Remix şarkı sözleri

Sanatçı: Salim Smart

albüm: Labarina Ep


Rub master
Haka so yake diba ya maida kai bawa
Matsayain ka bai duba ballai ya san kai waye
Ya sa ka kai jinya ka sauka ka kan hanya
Ka manta alkarya kayo kallar wawaye
A labarina
Soyayya tai mini garkuwa
A labarina
Soyayya ta sa dimuwa
A labarina
Soyayya ta sa shakuwa
A labarina
Nan ne ake gane kwanton bauna
La, labarina
La, labarina
La, labarina
La, labarina
Baka gane so, ya yake sai idan ya shige ka da karfi
Yai ma tambari a zuciya koko yai ma riko mai zafi
Baya uzuri nasan kasani kar ka ganni da laifi
Ko ba yau ba tabbas zaka fahimci naso ka ko watarana
La, labarina
La, labarina
La, labarina
La, labarina
A cikin kowa da akwai shi
Sannan baya tsufa, baya jin rarashi, bayan neman kofa
In zai shiga baka tarai shi, dan ba shi da wata suffa
Idanu basu ganin shi, balle kayi mai i'hisani
Bayin kaina ne ba
Kaima bayin kanka ba
Tsarin Allah neh, ba mai iya kauda shi
Ba wai matsiyi neh bah,sannan ba girma ne ba
Hallita ne, ba mai iya chanja shi
Bai barni bah, kaima bai bar ka ba
A zuciya shi ne ke sa rauni
So kenan, sanadin labarina
So kenan, sanadin labarina
So kenan, sanadin labarina
So kenan, sanadin labarina
Ahh, ah
Ahh, ah
Ahh, ah
Sanadin labarina!

Поcмотреть все песни артиста

Sanatçının diğer albümleri

Benzer Sanatçılar