Ni koh ina da wanda nake so Wanda kaunar shi tai mini naso Tinanin shi yai mini faso A idanu ya nai mini gizo Na kasa in furta so da baki Fafan rabe-rabe nakeyi a daki Na kasa bacci cikin tsanaki Ni so nakeyi kawai mu gana So ya sani jiri Ya sa nayi garari Yaki mini uzuri Ya sauya tinani na ♪ Ba da baki ake gane so ba Ba a bude zuciya a duba Inda so ya kaimu bamu je ba Amman mu dinga kyautata zato Ga masoyan mu kar mu dinga sa ran su kuna Na yarda ni da ke Na mika kai ga ke Ina ta ji dake Nima kiji dani Karki nisa dani Ki bini ko ina Kauna ta bi jiki Na zam miki mallaki Gari na ya fitar da tsaki Ke zaki zama uwar dana ♪ Duniya zata zam mini sabuwa Yanzu ne zan ji dadin rayuwa Sa kida zana tashi nayo rawa Tunda kai zaka zam ango na In ka kira ni gani Kowa ya sanka dani A kanka anyi dani Banji ko an ziga ni Burin da baka bani Kai zaka min izini In maka komai sila ta kauna Muyi rayuwar mu da kai Mutuwar mu tare da kai Ba mai raba ni da kai Muhadu aljanna