Kishore Kumar Hits

Auta mg boy - Amana Da Amana şarkı sözleri

Sanatçı: Auta mg boy

albüm: Amana Da Amana


Amana da amana da aminci
Idan so yakai so da karamci
Kisani sahun farko inyi wakilci
A zuciya in dauko soyayya

Ina da idanu bazanki na kalla ba
Masoyi na gaske bazai ki masoyi ba
Na mallaki baki ya bazan saki zance ba
Ki soni kawai tunda zuci ke tayiwa lamba
Jiya nayi mafarki
Gunki na zama sarki
Kinyi mini alkairi da zuciya kin bani
Idan da bukata aikenki ki aike ni
Zanyi miki gata tunda sanki ya raine ni
In zan tina baya wai a kanki a kere ni
Amfanin hakuri gashi ni na ciyo riba

Kece kika soni kin bar mini bashi
Kyawu fa akwai shi sai ma kin baza gashi
In dai kika barni tillas nayi toshi
Ina da bukatar nayi aure
Indai nashigo zan rufe kyaure
Ya zama halali akanki nayo kishi
Wakarki nake yi zo kiyi mini amshi
Kar so ya kasance tsuntsu mai tashi
Kece na rike zan saki kowa
Rashin ki kawai zanayi kewa
Dake zan zauna daram dam da amana

So ya zama kauna ki gane nufi na
Kaunarki nake yi nasaki a raina
Dake nayi yarda ki mallaki kaina
Jiki da jini so kin dada raina
Na baki guri fada zo shiga ki zauna
Gatan so yarda kinzo karni na
Ina miki zance kina dubi na
Madubin dubawa na dubin fuska na
Ina jin ki a raina kice zabi na
Yarda da aminci sune soyayya

Поcмотреть все песни артиста

Sanatçının diğer albümleri

Benzer Sanatçılar